Wani matashi dan shekara 21 da ake zargin yana shan kayan maye ya kashe iyayensa a karamar hukumar Nnewi da ke jihar Anambra.
Ana kiran sa da Chukwudi daga Nsukka a jihar Enugu.
Wanda ake zargin, wanda aka ce dalibi ne na daya daga cikin jami’o’in Anambra, Da daya tilo ne ga iyayensa, Mista da Misis Micheal Ulor.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa gawarwakin wadanda abin ya shafa sun fara rubewa ne a lokacin da aka gano su a gidansu da ke gidan Mista Moses Nnodu, Abubor Nnewichi-Nnewi, kusa da Kasuwar Orie Agbo, a yammacin ranar Alhamis.
KARANTA KUMA: Wata Tsawa Ta Kashe Jami’an Hukumar FRSC Har Guda Uku
An tattaro cewa wanda ake zargin ya kashe iyayensa ne bayan wata zazzafar muhawara kan kin ba shi wasu kudi.
A cewar mazauna yankin, Chukwudi ya kashe iyayensa inda ya gudu zuwa wani wuri da ba a san ko ina ne ba.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Daya daga cikin mazauna yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce makwabta ne suka gano gawarwakin, wadanda suka ji wani wari yana tashi.
Ya ce wanda ake zargin wani mutum ne da ya shahara wajen shan Miyagun kwayoyi na (Methamphetamine) a yankin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce rundunar ta kaddamar da farautar wanda ake zargin.
Ya ce, “Kwamishanan ‘yan sanda, CP Echeng Echeng, ya bayyana gano gawarwakin wadanda tuni suka rube a wani gida da ke Nnewi a ranar 22/9/2022 da misalin karfe 5:20 na yamma tare da yanka da adduna a jikin su.”
Ya kuma bayyana cewa, kwamishinan ya bayar da umarnin bin diddigin wanda ake zargin yayin da za a mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.
A wani labarin kuma: Sojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta A Dazukan Zamfara Da Katsina
Rundunar sojin saman Najeriya da ke aiki a jihar Zamfara ta kashe wani shugaban ‘yan bindiga, wanda aka fi sani da Dogo Rabe da wasu ‘yan kungiyarsa sama da 45 a dazuzzukan Zamfara.
Jami’an rundunar sojin saman Najeriya sun yi ruwan bama-bamai a sansanonin ‘yan bindigar da ke tsakanin al’umomin Zurmi da Birnin Magaji a jihar Zamfara da Jibia a jihar Katsina, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.