Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 37 tare da raba wasu 171,000 da muhallansu a jihar Adamawa a lokacin damina, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa (ADSEMA), Dr Muhammad Sulaiman ya bayyana.
Ya ce mutane 58 sun jikkata yayin da hekta 89,000 na gonaki ya nutse.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Sulaiman ya bayyana cewa ya shafi dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu wadanda suka hada da makarantu, asibitoci, kasuwanni, gidaje da wuraren ibada, wanda hakan ya shafi harkokin tattalin arziki da zamantakewa.
Ya koka da cewa ambaliyar ta wuce yadda hukumomin Najeriya suka yi hasashe wanda ya takaita ne kawai ga al’ummomin da ke gaba da gabar kogin Benue a jihar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ya ce hukumar ta raba kayan agaji ga daukacin sansanonin guda 10 da aka kafa domin ‘yan gudun hijira bisa umarnin gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Kano ta shirya bayar da gudunmawa ga aikin kidaya na ƙasa
Gwamnatin jihar Kano ta kuduri aniyar bayar da duk Wani goyon baya ga Hukumar kidaya t kasa, a yayin da ake Shirin Fara kidayar al’ummar Najeriya, a watan Afrilun sabuwar Shekara Mai shirin kamawa.
Mataimakin gwamanan Dakta Nasir Yusuf Gawuna ne ya bayyana haka a dakin taro na coronation hall dake gidan gwanna fadar Gwamnatin jihar.