Wata Daliba ta halaka kanta a jami’ar Fatakwal, da ke Babban Birnin Jihar Ribas, Dalibar mai suna Hikimat Gbadamosi, ta kashe kan ta ne Sakamakon Wata Kwaya da ta sha a dakin Kwanan Daliban da ke Jami’ar.
A tsinci Dalibar ne jiya a Dakinta kamar yadda babbar Aminiyar ta ta Sheda wa Manema Labarai cewa, Ana Zargin Marigayyiyar ta sha wata Guba ce Kwalba Biyu tun Ranar Asabar din da ta gabata.
Mun dauka ko dai ta yi tafiya ne domin mun nemeta ba mu ganta ba sai daga baya aka gane Ashe ma tana Dakinta rai yayi Halin sa.
Duk da dai Har ya zuwa Hada wannan Rahoton ba Wanda yasan dalilin me yasa Dalibar ta Kashe Kanta.