Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da sassauta dokar hana fitar da gwamnatin tarayya ta kafa a ranar 27 ga Afrilun da ya gabata. A yayin sanar da matakin sassauta dokar hana fita, Ganduje ya bayyana Litinin da kuma Alhamis, a matsayin ranekun da jama’a za su rika fita, amma daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.
Gwamna Ganduje ya ce kasuwannin ‘Yan Kaba da kuma Rijiyar Lemo kawai ne za su rika budewa a daukacin jihar, yayin da sauran manyan shagunan siyar da kayayyaki za su ci gaba da harkokinsu a ranekun da gwamnati ta baiwa jama’a damar fita.