Daga daga manyan Malaman Ahlussunnah Wal Jama’a shaikh Dakta Nura Khalid Yayi Allah wadai da wadanda suke danne hakkin talakawa a watan Ramadan, Inda ya bayyana su a matsayin azzalumai ne dukkan wanda zai karbi hakkin talaka na Shinkafar Korona kuma ya cinye.
Shaikh Nura Khalid ya bayyana hakan ne a wani faifain Bidiyo na ci gaba da Wa’azin Watan Ramadan mai albarka da yake gudanarwa a masallacinsa dake Bannex a babban birnin tarayyah Abuja.
“An baka abincin Korona ka raba ma mutane ka cinye kuma kazo kace a watan Ramadan watan yafiya ne, Allah mai gafarane zai gafarta maka, Waye zai yafe maka?
Allah ya yafe maka abinci Talaka daka cinye, ka wawure kudin talakawa kace wai Allah gafururraheem ne, eh Allah gafururraheem ne amma Takala ba gafururraheem bane.” Inji Shaikh Nura Khalid Abuja.