Wata kungiyar matasan yankin karamar hukumar Takum, ta jahar taraba, sun koka kan yadda rashin tsaro yayi kamari a yankin nasu.
Matasan sun bayyana hakan ne a hira da manema labarai a Abuja ta hannun Shugaban ta Irdomiya A Danjuma.
Wanda Yace Matsalar ta sanya da yawa sun bar yankin zuwa wani Yanki inda abun har ya shafi tattalin arzikin yankin na mu, inji shi.
Mazauna yankin suna cikin zaman dar dar inda suke gama harkokin su na yau da kullum a Karfe 7:00 na yammacin Kowace rana Dan kar wani Abu ya faru kamar Garkuwa da su, ya kara da cewa baki da mazauna duk a tsorace Mu ke inda sukayi kira ga jami’an tsaro da su dau mataki kan lamarin.