Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta ce ta shirya shirin wayar da kan alhazai na duk mako a cibiyoyi 16 na mahajjata na shekarar 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Sakataren zartarwa na hukumar, Ambasada Muhammad Abba-Danbatta, a wani taron manema labarai a Kano ranar Alhamis, ya ce za a fara shirin ne a tsakiyar watan Janairu.
A cewarsa, “shirin wayar da kan alhazai da za a yi jigilar su daga Najeriya zuwa Saudiyya a ranar 4 ga watan Mayu“.
KU KARANTA KUMA Hukumar Alhazan Kano Ta Ce Bata Fara Karbar Kudin Hajjin Bana Ba
Abba-Danbatta ya ce hukumar ta mayar da kudaden wadanda basu samu zuwa ba a bara kusan kashi 90 cikin 100 na mahajjata.
“Madodin kudin shine rarar Naira miliyan 2.5 da mahajjata suka biya a Hajjin 2022.
“Alhazan da suka ajiye kudi don aikin hajji za a ba su sabon rasiti don bude fayil, su fara aikin kuma su ne na farko da za a yi wa rijistar aikin Hajjin 2023,” in ji shi.
Abba-Danbatta ya ce hukumar za ta karbi ajiyar naira miliyan 1.5 don aikin Hajjin shekarar 2023 kafin hukumar alhazai ta kasa ta bayyana cikakken adadin kudin.
Ya kara da cewa masarautar Saudiyya ta soke kayyade shekaru da gwaje-gwajen da aka yi a yayin atisayen, inda ya ce za a duba takardar shaidar COVID-19 ne kawai idan za a je aikin hajjin. (NAN)/Solacebace.
A Wani Labarin Kuma Hukumar Fanshon Sojoji Ta Fara Biyan Masu Fansho, Da Na Wadanda Suka Rasu
Hukumar Kula da Fansho ta Sojoji a ranar Alhamis ta fara biyan ‘yan fansho da suka cancanta na soja da kuma dangin ’yan fanshon da suka rasu.
Shugaban hukumar Rear Adm. Saburi Lawal ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.