Wani faifan Bidiyon ya nuna yadda wata mata ta taba wata amarya a wuraren albarkatunta a wajen daurin aure a cocin dake Enugu-Ukwu, jihar Anambra, ya jawo hankalin amaryar.
Bayan an daura auren ango da amarya Mai Tsarki, baƙi sun tsaya a layi a kan dandamali don rungume su gami da gaisuwa don taya murna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Aure Akwai Daɗi, Na Sha Baƙar Wuya Lokacin Da Nake Gwauruwa -Wata Matashiya
A cikin wani faifan bidiyo da wani magidanci ya dauka, an ga wata bakuwa mace ta nufo amarya, Maimakon ta rungumi amaryar kamar yadda sauran baƙi suka yi, sai kawai matar ta miƙe ƙasa ta taɓa wurin da bai dace a jikin amarya.
Masu kallo sun nuna damuwa, inda da yawa ke tambayar dalilin da yasa matar ta taba wurin da bai dace na kowane wuri.
A wani labarin kuma, Hukumar Fanshon Sojoji Ta Fara Biyan Masu Fansho, Da Na Wadanda Suka Rasu
Hukumar Kula da Fansho ta Sojoji a ranar Alhamis ta fara biyan ‘yan fansho da suka cancanta na soja da kuma dangin ’yan fanshon da suka rasu.
Shugaban hukumar Rear Adm. Saburi Lawal ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.