Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya sanya dokar hana fita daga garin Lambata da ke karamar hukumar Gurara a jihar sakamakon wani kazamin rikici da ya kai ga kashe Hakimin kauyen Mohammed Abdulsafur.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Ahmed Matane ya fitar ranar Lahadi a Minna.
KU KARANTA KUMA Yan Sanda Sun Musanta Sanya Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomin Biyu Na Neja
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, wasu ‘yan daba sun kashe hakimin kauyen Lambata a ranar Asabar a wani rikici da ya barke.
Mista Sani Bello ya bayar da umarnin sanya dokar hana fita a garin daga karfe 6.00 na dare zuwa karfe 6.00 na safe, daga ranar Lahadi, har zuwa wani lokaci.
Ya ce, sanya dokar ta-bacin ya zama dole domin a taimaka wa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura, da ceton rayuka da kuma maido da doka da oda.
A cewar gwamnan, gwamnati ta yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da rashin bin doka da oda da suka faru a garin Lambata.
Ya yi kira ga al’ummar yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai domin dawo da zaman lafiya a garin, ya kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana fitar. NAN/Solacebace
A Wani Labarin Kuma Gwamnatin Kano Ta Musanta Rahotannin Cin Zarafin Yara A Gidan Marayu
Gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da rahoton zargin cin zarafin yara da jami’anta suka yi a gidan yara na maratu da ke Nasarawa.
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Dakta Zahra’u Muhammad-Umar, ta yi watsi da rahoton yayin da take zantawa da manema labarai a Kano ranar Lahadi.