Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta mayar da martani kan abin da ta kira wani labarin karya da ke yawo a wasu shafukan sada zumunta na yanar gizo, wanda ke nuni da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a shingen binciken sojoji da ke Zuma Rock, kuma an samu kwararar ‘yan bindiga da dama a jihar ta Neja ta Birnin Yankin Gwari.
A cewar sanarwar da kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, CP Ogundele J. Ayodeji ya fitar, rahoton karya ne ya ci gaba da cewa DPO/DSS na karamar hukumar Rafi ya tabbatar da babu irin wannan yunkuri na ‘yan bindiga cikin jihar.
Rundunar ta bayyana ba tare da wata shakka ba cewa rahoton bashi da tushe balle makama, inda ya kara da cewa kawai hasashe ne na masu yin barna wadanda manufarsu ita ce haifar da firgici a cikin al’umma ta hanyar samo irin wannan rahoton.
KU KARANTA KUMA Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita A Yankunan Rafi Da Shiroro
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Sanarwar ta kuma kara da cewa wasu bayanai da ke nuna cewa irin wannan rahoton karya ne, “bangaren da ya bayyana cewa an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Kagara.
“Ya dace a bayyana cewa ba a sanya dokar hana fita ko wace iri a Kagara ba, babu wani rahoto da ya fito daga DPO da DSS a karamar hukumar Rafi, haka ma babu wani rahoton ‘yan bindiga sun kai hari a Dutsen Zuma, Suleja”.
Kwamishinan ya kuma bukaci jama’a da su yi watsi da irin wannan labarin na kage, su ci gaba da gudanar da sana’o’insu ba tare da fargaba ko tsorata, cin zarafi ko kowane irin hari ba.
Saboda haka ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar “suna bakin kokarinsu wajen ganin an tabbatar da cewa an tabbatar da tsaro a jihar da muhalli mai aminci”.
Bugu da kari, rundunar ta ce ta na sane da yadda ‘yan ta’addan ke aiwatar da ramuwar gayya, saboda wasu nasarorin da aka samu a kan ‘yan ta’addan a lokacin da suke gudun hijira a jihar.
Ya kara da cewa an bullo da dabarun dakile irin wannan yunkuri, tare da yin kira ga ‘yan bindigar. ‘Yan Neja su ma su ci gaba da tallafa wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da sahihan bayanai domin samun damar shiga tsakani cikin gaggawa.
A wani Labarin Kuma Tinubu Ya Yi Alkawarin Mayar Da Kudu Maso Gabas Kamar Taiwan
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tare da abokin takararsa, Mista Kashim Shettima, a ranar Alhamis sun mamaye jihar Ebonyi, inda tawagar yakin neman zaben jam’iyyar suka tsaya.
A Ebonyi, “Sinadarin Al’ummarmu”, Tinubu ya nanata imaninsa ga ruhin kasuwanci wanda shine alamar Kudu maso Gabas.