Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane da ake zargi da mallakar muggan makamai, satar mota da sauran miyagun ayyuka a jihar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya ce rundunar ta yi aiki da sahihan bayanai domin kama wadanda ake zargin.
Sanarwar ta ce, ‘yan sandan da ke aiki da shedkwatar ‘yan sanda na Toro a lokacin da suke sintiri a kusa da kauyen Nabardo, sun kama wani Umar Abubakar mai shekaru 21 da haihuwa da laifin sayen bindiga samfurin cikin gida.
KU KARANTA KUMA Gwamnan Baichi Na Shirin Yin Watsi Da Tafiyar Atiku Abubakar
An ce wanda ake zargin ya samu makamin ne a hannun abokinsa Mohammed, wanda ya fito daga jihar Nasarawa.
Sanarwar ta kuma ce, ‘yan sandan sun kai samame maboyar ‘yan ta’adda a karamar hukumar Alkaleri tare da kwato wasu bindigu guda biyu.
“A wani ci gaba mai alaka da shi, a ci gaba da aikin da ake yi a yankin Alkaleri, jami’an ‘yan sanda da ke shedikwatar ‘yan sanda na Alkaleri, sun gudanar da bincike kan bayanan sirri tare da kai samame a maboyar wani mai laifi da ke tsaunin Kashereyel kusa da gundumar Gwana a karamar hukumar Alkaleri.
“A yayin farmakin, an gano bindigar Pump-Action ta Ingilishi guda daya,” in ji sanarwar a wani bangare.
A wani labarin makamancin haka, rundunar ‘yan sandan jihar ta kuma ce ta kama wani mai suna Abdul Mohammed da ake kira da P. A da ke garin Karofi Bauchi a jihar Bauchi da hannu a satar wata mota kirar TOYOTA COROLLA LE mai lamba NSR-510TY mai launin ash.
“Da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya karbi motar ne daga wani mai suna Haruna wanda ba a san shi ba a garin Biu, karamar hukumar Biu, ta jihar Borno, wanda a yanzu haka an kai shi ga wani Ibrahim Babaji mai shekaru 30 a garin Misau.
Sanarwar ta kara da cewa, karamar hukumar Misau, jihar Bauchi, wanda shi ma aka kama shi kuma ya amsa cewa ya sayi motar ne daga hannun wani Barau Alim Tela mai adireshi daya, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.
Sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi CP Aminu Alhassan yayin da ya yaba wa jami’an rundunar bisa nasarar da aka samu, ya kuma ba da tabbacin cewa za a fito da duk wasu masu aikata laifuka daga maboyar su kuma za su amsa laifukan da suka aikata a lokacin da ya dace.
A Wani Labarin Kuma Fira Ministar Kasar New Zealand Ta Yi murabus Daga Matsayinta
Firaministar Kasar New Zealand Jacinda Ardern, shugabar cigaban siyasar duniya, ta girgiza kasar a ranar Alhamis inda ta ba da sanarwar yin murabus daga mukaminta cikin makwanni kadan.
‘Yar shekaru 42 – wacce ta jagoranci kasar ta bala’o’i, cutar sankarau, da kuma mummunan harin ta’addanci – ta ce ba ta da “shugabancin ya isa”.