Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi zai yi watsi da bangaren Atiku a hukumance, tare da komawa bangaren gwamnonin G5. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A cikin wasikar da ake “zargi” ya aikewa Shugaban Jam’iyar na kasa Iyorchie Ayu an yi kirarin ya ce, “Da yuwuwar na aje matsayina a kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa domin in samu natsuwar samar da wasu matakai da tsare tsaren da ka iya taimakawa dukkanin yan takarar jam’iyar PDP da ni kai na, wajan lashe zaben dake tafe, idan ba a magance matsalar da ake fuskanta ba.”
A wani labarin kuma, Gwamnonin G-5 Za Su Kira wa Atiku Ruwa, Za Su Ziyarci Wani Gwamnan Arewa
A dai dai lokacin da wasu masu ruwa da tsaki ke ƙoƙarin shawo kan rikicin da ya da baibaye jam’iyar PDP Kafin zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe a ranar 25 gawatan Febuwairun shekarar 2023, rukunin gwamnonin nan a jam’iyar ta PDP wato G-5, sun shirya zuwa Bauchi domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen gwamna Bala Muhammad karo na biyu.
.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa bisa samun rashin jituwa tsakanin Gwamna Bala Muhammad da wasu ‘yan siyasa na hannun daman Atiku Abubakar, Gwamnan ya yanke shawarar kulla alaƙa da Rukunin Gwammnonin G-5 domin samun sai’da.
Wata majiya dake kusa da yan ƙungiyar ta tabbatar cewa gwamnonin guda biyar na Shirye shirye-shiryen zuwa Bauchi domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Gwamna Bala Muhammad da aka tsara ƙaddamar wa a ranar Laraba.
Majiyar ta ƙara da cewa gwamnonin zasu wuce Ibadan Babban Birnin jihar Oyo daga Bauchi domin ƙaddamar yaƙin neman zaɓen ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar su wato Gwamna Seyi Makinde wanda aka tsara gudanarwa a ranar 5 ga watan Janairu.
Duk kuwa da cewa bai ayyana shiga cikin kuñgiyar ta G5 ba , Bala Muhammad yana da tsamin dangantaka tsakanin sa da Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyar PDP Atiku Abubakar, inda ya zargi Atikun da magoya bayan sa da cewa suna aiki don ganin bai sake lashe zabe ba.