Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ta raba magunguna ga asibitoci hudu a jihar Kano domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da sauran abubuwan gaggawa.
Da yake gabatar da kayayyakin, babban daraktan hukumar NEMA, Mustapha Habib-Ahmed, ya ce kungiyar Map International ce ta bayar da tallafin ga asibitocin Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Wasu Dattawa a Arewa, Mu Gwamnonin Arewa Mune Dattawan – El-Rufai
Habib-Ahmed, wanda ya samu wakilcin ko-odinetan hukumar NEMA a ofishin reshen Kano da Jigawa, Nuraddeen Abdullahi, ya ce an bayar da tallafin ne domin kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya na samar da ingantaccen kiwon lafiya ga wadanda ambaliyar ruwa, garkuwa da mutane da ‘yan fashi suka shafa.
Ya lissafa asibitocin da suka amfana da su ka hada da asibitin kwararru na Murtala Muhammad, babban asibitin Bichi, babban asibitin Wudil, da babban asibitin Karaye.
Wasu daga cikin abubuwan da aka rarraba sun haɗa da micronutrient na haihuwa X100, sirinji, man krill 500mg, gilashin ido, abun numfashi, lancet pro-care, abin feshin ƙwayar cuta, rigar shingen da za a iya zuba abu mai kaifi da sauransu.
A nasa jawabin, gwamna Abdullahi Ganduje ya godewa hukumar NEMA bisa wannan tallafin, sannan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su tabbatar da yin amfani da kayayyakin cikin adalci.
Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, Saleh Jili, ya yi kira da a ci gaba da hada kai tsakanin SEMA da NEMA.
Ya shawarci jama’a musamman mata masu amfani da itace, da iskar gas, da gawayi da su rika kula da wuta tare da kashe na’urorin lantarki a duk lokacin da ba a amfani da su.
Gwamna Ganduje ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su daina zubar da shara ba tare da kakkautawa ba, sannan kuma su rika share magudanun ruwa domin kaucewa ambaliya.
Da yake mayar da martani, daraktan hukumar kula da asibitocin jihar Kano, Nasiru Alhassan-Kabo, ya yabawa hukumar NEMA bisa wannan karimcin.
Alhassan-Kabo, wanda mataimakin daraktan hukumar kula da asibitoci, Ibrahim Abdullahi ya wakilta, ya ce asibitocin za su tabbatar da amfani da kayan aikin yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, Messi Ya Tabbatar Da Zai Koma Barcelona
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Lionel Messi ya tabbatar da cewa zai koma Barcelona a nan gaba idan ya kammala wasansa.
Messi, wanda ya bar kungiyar ta Catalonia zuwa PSG a bazarar 2021, ya bayyana Barcelona a matsayin gidansa.