Hukumar ci gaban arewa maso gabas, NEDC ya bayyana aniyarta na samarwa da ‘ya gudun hijira gidaje dubu goma a jihar Borno.
Alhaji Mohammed Alkali, Daraktan hukumar ta NEDC shi ne ya bayyana hakan a yayin bude taron tallafin shugaban kasa Muhammadu Buhari a Ngom dake karamar hukumar Mafa a jihar a ranar Juma’a.
Alkali ya ce gina gidajen nan zai taimaka wajen shawo matsalar rashin wurin zama ga ‘yan gudun hijira. Ya bayyana cewa akalla kashi shida na gidaje a jihar Boko Haram sun tarwatsa su. Inda ya kara da cewa; dukiyar da muhallan da Boko Haram suka tarwatsa ya kai Dala biliyan 9.6.