Majalisar dinkin duniya a cikin sabon rahotonta kan abinci da yunwa a fadin duniya ta ce mutane da yawa na shiga matsalar yunwa.
Cikin rahoton da ta fitar ranar Litinin, ta ce akalla mutum miliyan 687.8 suka shiga matsanancin yunwa a 2019, inda aka samun karin miliyan 10 idan aka duba 2018.
A cewar binciken, tsadar rayuwa na daga cikin abin da yasa jama’a da dama basa iya cin abinci lafiayye ba.
Ta kuma yi gargadi, idan WHO ya yi sake yunwa yazo ko ina, zuwa karshen 2020, wadanda za su yi, fama da yunwa mutun miliyan 130.
Asia ke kan gaba cikin nahiyoyin dake fama da yunwa, mutum miliyan 381, inda a Afrika ke farar nemn
Sai kuma kasashen a yankibn Latin Amerika, inda yunwa ke jikin mutum 58.
Alkaluman sun nuna cewa yunwa ya karu da da kashi 8.9 % tun 2014.
A cikin wani faifan bidiyo, Sakataren Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterrsres ya nuna damuwarsa kan rahoton.
“Idan dai a duniyar nan ne, yunwa ya yi kaka-gida kuma kullum kara yawa yake.
“Kasashe na ci gaba da fama da rashin abinci. Annobar cutar korona na kara munin lamarin,” inji Guterres.
Ya ce yakamata duniya ta dauki mataki don kare karin jama’a daga shiga cikin yunwa.