Hukumar dake kula da birnin tarayya Abuja, FCTA ta bayyana aniyarta na bunkasawa masu gudanar da kananan sana’o’i a birnin.
Ministan Abujan, Malam Muhammad Bello shi ne ya yi wannan alkawarin a yayin da yake karbi bakuncin wasu kungiya da suka karrama shi a ofishinsa dake Abuja a ranar Talata.
Bello ya ce masu gudanar da kanana da matsakaitan sana’o’i suna taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasarnan.