Burin Cristiano Ronaldo na zama dan wasa mafi yawan kwallaye a Turai a bana, ya gamu da cikas bayan ya gaza jefa kwallo ko guda a wasan da kungiyarsa ta Juventus ta sha kashi da ci 2-0 a hannun Cagliari a gasar Serie A.
Dan wasan ya samu nasarar jefa kwallaye 31 a gasar Serie A ta Italiya a kakar bana, amma ya shiga halin damuwa a karawar da suka yi da Cagliari a daren ranar Laraba.
Ronaldo na biye da Ciro Immobile na Lazio wanda ke da yawan kwallaye 35 da ya zura a raga.
A ranar Laraba ne Immobile ya ci kwallonsa ta 35 a wannan kaka a wasan da kungiyarsa ta Lazio ta doke Brescia da ci 2-0.
Sai dai Immobile bai goge tarihin da Gonzalo Higuain na Napoli ya kafa ba a kakar shekarar 2015-16, inda ya zama dan wasa mafi yawan kwallaye a cikin kaka guda a tarihin gasar Serie A.