Alarammomi a Kaduna sun zabi Uba Sani wanda zasu marawa baya
Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Kaduna a karkashin Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya yi taro da Gamayyar Ƙungiyoyin Alarammomi da Maluman Tsangaya a Jihar Kaduna.
A lokacin taron, Gamayyar Ƙungiyoyin sun ce sun zaɓi Uba Sani da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin ƴan takarar su da zasu marawa baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Yiwa Najeriya Aiki Tukuru Kamar Yadda Buhari Ya Yi – Tinubu
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ɗan Takarar Gwamnan Uba Sani ya fitar a shafin sa na Facebook, da Jaridar Dimukuradiyya ta samu.
A cewar sa na halarci Gagarumin taro na Ƙungiyar Alarammomi da Maluman Tsangaya a matsayin Babban bako na suka goyi baya na da Tinubu.
Yace “na halarci taron Ƙungiyoyin Alarammomi da Maluman Tsangaya na Jihar Kaduna a matsayin Babban bako. A lokacin taron, Gamayyar Ƙungiyoyin Almjirai dana Tsangaya a Kaduna sun goyi bayan takara ta, da ta Asiwaju Bola Tinubu da sauran ƴan takarar APC a Jihar.