Mambobin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun yi kira da a kafa wani shiri mai dorewa ga tubabbun ‘yan ta’adda a yankin.
Sun yi wannan kiran ne a wajen taro na shida na dandalin tattaunawa a ranar Talata a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Gwamnonin sun tattauna batutuwan ta’addanci, garkuwa da mutane, rikicin manoma da makiyaya, da dai sauran kalubalen da yankin Arewa maso Gabas ke fuskanta.
“Kungiyar ta yi la’akari da cigaban da aka samu a harkar tsaro a yankin kamar yadda ya nuna yadda mayakan Boko Haram suka mika wuya tare da yabawa Gwamnatin tarayya kan shirye-shiryenta daban-daban na tabbatar da zaman lafiya a yankin,” in ji sanarwar da aka fitar a karshen taron, shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.
“Duk da haka, kungiyar ta bukaci a kafa wani shiri mai dorewa domin tunkarar ‘yan ta’addan da suka tuba. Kungiyar ta lura cewa sace-sacen mutane da rikicin manoma da makiyaya da dai sauransu na da matukar tayar da hankali a yankin kuma an yanke shawarar daukar matakan da suka dace don dakile matsalar.”
Baya ga batun tsaro, gwamnonin sun tattauna ne a kan gabatar da jawabin da ministan wutar lantarkin ya yi kan ayyukan da aka tsara da kuma ayyukan da ake yi a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya bayyana kalubalen da ke tattare da cigaba da samar da wutar lantarki a yankin.
Har ila yau, sun koka da rashin wutar lantarki na kusan shekara guda a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da kewaye, inda suka bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da mafita mai dorewa.
Gwamnonin sun kuma nuna damuwarsu kan rashin gudanar da ayyukan samar da wutar lantarki na Dadin Kowa da Kashimbila da suka ce yana kawo cikas ga cigaban yankin. Sun kuma shawarci Gwamnatin tarayya da ta kara zuba jari a yankin Arewa maso Gabas domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban tattalin arziki.
Sanarwar ta kara da cewa “Majalisar ta yi shawarwari sosai kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.” “Ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da Gwamnatin tarayya da su samar da isasshen kudi a cikin kasafin kudin shekarar 2022 don aiwatar da aikin.
“Kungiyar, yayin da ta fahimci cewa kasafin 2022 yana kan matakin ƙarshe, yana kira ga Majalisar Dokoki ta kasa da ta dubi yankin da kyau da nufin ganin an samar da isassun kasafin kuɗi na dukkan manyan ayyuka a yankin. .”
A cikin kudurorinsu, sun amince da gudanar da taron na gaba daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Maris, 2022 a jihar Gombe.
Gwamna Zulum, da Gwamna Inuwa Yahaya Gombe, da Gwamna Mai Mala Buni Yobe sun halarci taron yayin da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, da Gwamna Darius Ishaku na Taraba, mataimakansu suka wakilce su.