Hukumomi bayyana cewa sama da mutane sittin aka kashe a hare -haren da aka kai a fadin Arewacin kasar a ‘yan kwanakin nan.
Sannan sun kara da cewa sama da mazauna kauyuka talatin ne suka mutu a wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.
Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari garuruwa biyar tare da kona sansanonin soji a Sokoto arewa maso yammacin kasar. Sun kashe jami’an tsaro goma sha bakwai da fararen hula biyu.
Kazalika, a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, sojoji da ‘yan banga sun mutu lokacin da ‘yan Boko Haram suka harba rokoki kan ayarin motocinsu sannan motar sojoji ta bi ta kan wani abu mai fashewa