Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, LP, a zaben shugaban kasa da ya gabata, Mista Peter Obi, a ranar Lahadi ya ce ana yi masa barazana saboda kin amincewa da tayin da aka yi masa.
Obi ya ci gaba da cewa a shirye yake ya kasance a kowane irin yanayi muddin akan ra’ayin da yake kanshi ne.
Karanta nanJanyo hankalin masu zuba jari ya kamata muyi daga kasashen waje ba korar su ba – Peter Obi
Tsohon gwamnan jihar Anambra bai bayyana sunayen mutane ko kungiyoyin da suka yi masa barazanar ba.
Ya yi wannan da’awar yayin gabatar da tambayoyi a matsayin bako akan wani shiri na X Space wanda “ParallelFacts” ya shirya.
Obi ya dage cewa ba ya tsoron mutuwa kuma zai kasance a kan hanya madaidaiciya.
Zan iya gaya muku tayin da nake samu a yau yana da ban tsoro,kuma don naki karbar tayin, abin da suke so su yi mini shi ma yana da ban tsoro amma a shirye nake in shiga ta kowane hali.
Kamar yadda na ci gaba da gaya wa mutane, sa’ad da suke cewa,Obi kana sa ranka cikin haɗari’, idan na mutu da shekaru sittin, ban mutu a matashi ba.
A wani labarin kumaNLC, PDP, LP sun yi wani gargadi bayan Bankin Duniya ya ba da shawarar maida lita 750
Wasu mutane sun mutu a cikin shekaru ashirin, talatin da arba’in kuma ina da ’ya’yan da yanzu sun kammala karatunsu kuma suna yin abubuwan da suka dace.
Idan na mutu a yau hakan yayi matukar ban kauce daga wadannan abubuwan da na fada ba tun ranar da na yanke shawarar shiga gwamnati.
A kowane lokaci a kowane minti ina fatan in kasance a kan hanya madaidaiciya, in ji Obi.