A yau Kotun koli za ta raba gardama a jihohin Kano, Plateau, Legas, da wasu 4
A yau ne kotun koli za ta yanke hukunci kan kararrakin da aka yi na gwamna a jihohin Kano, Plateau, Lagos, Zamfara, Ebonyi, Bauchi da Cross River.
A cikin jahohin bakwai, na Kano da Filato ne suka fi kowa rigima.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wani Babban Makusancin Gwamna Zulum Ya Mutu
Kano
A Kano, shari’ar tana tsakanin Gwamna Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP, da Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC.
A watan Satumba ne wani kwamiti mai mutane biyar karkashin jagorancin Mai shari’a John Okoro ya soke nasarar da gwamna Yusuf ya samu a zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris tare da tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin zababben gwamnan Kano.
A ranar 13 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun ta yanke, inda ta ce tsige Abba Yusuf ya yi daidai saboda bai cancanta ya tsaya takara ba. Amma gwamnan ya garzaya zuwa kotun koli domin neman hakkinsa.
Plateau
A ranar 9 ga Janairu, 2024, Kotun Koli ta tanadi hukunci a cikin karar da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya shigar, na neman soke hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke wanda ya soke zabensa.
Wani kwamitin alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a John Okoro ya ajiye hukunci bayan sauraron hujjojin da jam’iyyu suka yi akan karar da aka shigar.
Gwamnan ta bakin lauyansa, Kanu Agabi, ya roki kotun da ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, sannan ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara saboda wadanda ake kara ba su da hurumin yin tambaya kan yadda jam’iyya ke zaben shugabanninta na jihohi.
Ya ce wadanda ake kara ba za su iya cewa gwamnan bai ci adadin kuri’un halal da aka ba shi ba a daidai lokacin da suka ce zaben bai inganta ba.
A watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori Mutfwang tare da umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta ba Goshwe takardar shaidar cin zabe amma gwamnan ya garzaya kotun koli domin neman hakkinsa.
A wani labarin kuma:Wani Babban Makusancin Gwamna Zulum Ya Mutu
Mallam Isa Gusau, kakakin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya rasu.
Gusau, wanda kuma shine kakakin mataimakin shugaban kasa na yanzu, Sanata Kashim Shettima, lokacin yana gwamnan jihar Borno, ya kwashe sama da wata guda yana jinya a wani asibitin Indiya.