Kwamitin karbar mulki na gwamnan Kano mai jiran gado Abba Kabir Yusuf ya bukaci al’ummar jihar Kano, da su taimakawa gwamnati mai jiran gado da bayanai game da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban kwamitin Dr. Baffa Bichi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai a birnin Kano.
KU KARANTA: Yan Najeriya Na Daya Daga Cikin Masu Kwasan Garabasa Wajan Siyan “Data” A Duniya — Rahoto
Sanarwar ta nemi duk wanda ke da wasu muhimman bayanai kan yadda aka gudanar da gwamnatin Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023, zai Iya mika bayanan, kau tsaye ga shalkwatar kwamitin karbar mulkin dake Tahir Guest Palace, lamba. 4 Ibrahim Natsugunne Road.
“Haka kuma zai iya aike da bayanan ta wannan adireshin Gmail: GTC2023@gmail.com”. A cewar sanarwar
Wannan na zuwane yayin da ya rage kwanaki 11 a rantsar da sabuwar gwamnati a Kano da matakin Kasa baki daya.
A wani labarin kuma: NNPP Bata Da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu A Kotu – Buba Galadima
Buba Galadima, ya ce jam’iyya NNPP ta ki kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa a 2023 a kotu saboda rashin kudi. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ARISE TV kan ganawar da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya yi da zababben shugaban kasa, Tinubu.
Daily Trust ta ruwaito wata ganawar da Tinubu da Kwankwaso suka yi a birnin Paris na kasar Faransa, wanda abokin Kwankwaso kuma tsohon kodinetan yakin neman zaben Tinubu, Abdulmumini Jibrin, kana zababben dan majalisar wakilai da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP daga APC kafin babban zabe ya shirya.