Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce gwamnati mai zuwa a Kano za ta sake duba batun tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 14.
Sanusi wanda ya zama sarki a wa’adin karshe na Kwankwaso a matsayin gwamna, Gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ne ya tsige shi, wanda shi ne mataimakin gwamna a lokacin da aka nada sarkin.
KU KARANTA: Ranar Ma’aikata: NLC, TUC Sun Yi Allah Wadai Da Matakin FG
An cire Sanusi ne a ranar 9 ga Maris, 2020, sannan kuma an kore shi daga Kano aka aike da shi zuwa Loko, wani yanki mai nisa a jihar Nasarawa, yayin da ake binciken kudaden masarautar da ke karkashinsa.
Ganduje ya kuma raba masarautun gida biyar ya nada sarakunan masu daraja ta daya.
Sai dai da yake magana a wani faifan bidiyo Kwankwaso ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf, zababben gwamna, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, zai duba batun tsige sarkin.
Ya kuma yi addu’ar samun taimakon Allah ga Gwamna mai jiran gado, domin samun damar tafiyar da al’amura cikin sauki.
Ya yi magana ne a wajen gabatar da wani littafi kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda wani dan jarida, Mista Bonaventure Melah ya rubuta.
Ganduje ya ce Sanusi ba shi ne mutumin da ya fi dacewa da karagar mulki ba, yana mai zargin cewa an nada tsohon sarkin ne domin ƙuntatawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
A watan Afrilun 2014 ne Jonathan ya tsige Sanusi daga mukamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) saboda ikirarin da tsohon gwamnan CBN ya yi cewa wasu mutane a karkashin gwamnatin Jonathan sun sace dala biliyan 49.
Da yake nuna rashin jin dadinsa kan yadda Sanusi ya fito fili kan badakalar da ake zarginsa da aikatawa, Ganduje ya ce ya kamata tsohon gwamnan na CBN ya tattauna batun a asirce da tsohon shugaban kasar wanda shi kuma zai iya ba da umarnin gudanar da bincike kan zargin.
A wani labarin kuma: Sudan: FG ta Fitar Da Bayani Kan Kwaso Yan Najeriya Daga Masar Da Suka Makale
Gwamnatin tarayya ta ce an share jirgin saman Najeriya NAF C-130H da jirgin Air Pace a Masar domin kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan.
Gwamnatin ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwar hadin gwiwa da Sakatarorin Ma’aikatar Harkokin Waje, Ambasada Janet Olisa, da na harkokin jin kai, Dr Sani Gwarzo a Abuja.