Tsohon dan majalisa kuma fitaccen mai sukar lamirin gwamnatin Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa zabe mai guba ne ke haddasa rugujewar dimokuradiyya a Afirka.
Kalaman Sani na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi juyin mulki a kasar Gabon dake Afirka ta Tsakiya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa da sanyin safiyar yau ne jami’an soji a Gabon suka sanar da kwace mulki bayan sake zaben shugaba Ali Bongo Ondimba a karo na uku.
Rahotanni sun ruwaito cewa manyan hafsoshin sojin kasar ne suka bayyana hakan a ranar Talata a babban gidan talabijin na kasar.
KARANTA NANYa Kamata A Dauki Mataki Kan Yawaitar Juyin Mulki A Afirika–Tinubu
An bayar da rahoton cewa, jami’an sun sanar da soke sakamakon zaben na ranar Asabar da ‘yan adawa suka yi watsi da su tare da bayyana shi a matsayin zaben shugaban kasa mai cike da magudi.
Sai dai Sani, a wani sako da ya wallafa ta dandalinshi na sada zumunta na X, ya zargi iyalan Bongo da mamayar da ruguza dimokradiyya a Gabon.
Ya rubuta cewa mutane a Gabon sun fito suna yin zanga-zanga kan tituna don nuna goyon bayan juyin mulkin da aka yi a Libreville. Iyalan Bongo sun mamaye kuma sun ruguza Dimokradiyya. Dimokuradiyya na mutuwa a Afirka muddin anayin zabe mai cike da magudi.
Kuma muddin idan har za’a cigaba da yin murdiya wajen gudanar da zabe a kasashen Afirika to ba za’a daina ganin sojoji na karbe mulki daga hannun zababbun shugabannin kasashe ba.
A WANI LABARIN KUMA
Fiye Da Daliban Firamare Miliyan 4 Ne Basuda Kujerun Zaman Aji A Jahar Kano-Kwamishinan Ilimi
Kwamishinan Ilimi Na Jahar Kano Umar Haruna Doguwa ya bayyana damuwa akan halinda Jahar ke ciki ta fannin Ilimi inda ya bayyana hakan a matsayin babban abin kinya da jahar ta tsinci kanta sakamakon sakacin da tsohuwar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi.