- Shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa Farfesa Abubakar Rasheed a ranar Litinin ya sanar da yin murabus
- Shugaban hukumar ta NUC yayi murabus, ya yin da ya koma aikinsa na asali
- An nada Rasheed a matsayin shugaban NUC shekaru bakwai da suka gabata a zamanin tsohon ministan ilimi
Shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa Farfesa Abubakar Rasheed a ranar Litinin ya sanar da yin murabus bisa radin kansa.
Rasheed ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu inda ya ce zai koma Jami’ar Bayero Kano domin ci gaba da aikinsa na koyarwa.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: FG Ta Ayyana Ranakun Hutun Babbar Sallah
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa an nada Rasheed a matsayin shugaban NUC shekaru bakwai da suka gabata a zamanin tsohon ministan ilimi, Malam Adamu Adamu.
A lokacin da yake rike da mukamin shugaban NUC, hukumar ta amince da mafi yawan jami’o’i masu zaman kansu.
Tsarin jami’oi ya kuma shaida yadda aka samu mafi yawan ayyukan masana’antu.
A wani labarin kuma,Karya Ta Kare: EFCC Ta Yi Caraf Da Sanata Kan Damfarar Makudan Kudi
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kama wani sanata na jabu, Ifechukwu Makwe bisa zargin zamba cikin aminci ta intanet €5.7m.
An kama Makwe ne a unguwar Guzape da ke Abuja, biyo bayan wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan damfarar sa ta intanet.