Wata kungiya mai goyon bayan takarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaben da ya gabata ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya baiwa tsohon gwamnan Jahar Zamfara.
Dake Arewa maso yammacin Najeriya Dr Bello Matawallen Maradun kujerar Minista domin daidaito a cikin mulkinsa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito kungiyar goyon bayan Asiwaju ta Arewa ta tsakiya na cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a matsayin minista domin ya nuna a shirye ya ke na kafa gwamnatin hadaka.
KARANTA NANDalilin Da Yasa Majalisar Ta Ki Tabbatar El-Rufai, Danladi Da Okotete A Minista — Akpabio
Shugaban kungiyar na kasa, Abba Rios Lawal, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, ya ce nadin Matawalle mataki ne da ya dace ya kuma yi fintinkau a adalci
Hakan ya faru ne yayin da suka bi sahun takwarorinsu na wasu shiyyoyin domin taya Matawalle murna tare da yaba wa Tinubu kan zaben da ya yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ba za mu iya mantawa da gagarumin goyon baya da kwarin gwiwa da aka ba mu a duk lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na Asiwaju ba.
Matawalle ya ba mu goyon baya duk da cewa shi ba dan shiyyar Arewa ta Tsakiya ba ne, kuma aikin sa ya takaita ne kawai a Kudu maso Yamma.
A zabin Matawalle, shugaban kasa ya nuna hikima da hangen nesa kuma ba tare da wata shakka ba, za mu iya da karfin gwiwa cewa zai yi farin ciki da abinda yayi.
Kungiyar ta kuma taya Alhaji Abdullahi Umar Ganduje murnar hawansa kujerar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na kasa.
Wannan wata hujja ce da ke nuna cewa Shugaba Tinubu babban jigo ne amintacce wanda ya tsaya tsayin daka kan kalamansa duk da cewa akwai matsala.
Da haka ne kungiyarmu ta yanke shawarar neman izinin kai wa sabon shugaban kasa ziyarar ban girma da kuma jajircewarsa ga jam’iyyar APC.
A WANI LABARIN KUMA
Ku Biya Haraji Don Ni Bazan Ciwo Bashi Don Yin Aiki Ba-Tinubu Ga Yan Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu Na Najeriya ya bukaci yan kasar da su daure su dinga biyan haraji domin samun kudin gudanar da wasu manyan aiyuka a kasar inda ya kara da cewa shi ba zai iya cin bashi domin gudanar da manyan aiyuka ba