Ministan shari’a na kasa Abubakar Malami ya ce ko kadan ofishinsa bai wanke Abba Kyari daga zarge zargen da ake yi masa ba.
Ya ce kafafen yada Labarai ne kawai suka canja masa kalamai.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Jami’in yada labaransa Dr Umar Gwandu ya fitar da yammacin yau Lahadi.
Ya ce da alama jama’a basu fuskanci kalamansa na baya ba, yan jarida kuma suka yadawa jama’a ba dai-dai ba.
Ya ce ofishin attorney janar din ya bayar da dama ne da a kara tsananta bincike kan wasu zarge zargen da ake yiwa Abba Kyarin.
Gwandu ya ce har yanzu ofinshin attorney janar bai yanke wata matsaya akan mas’alarba, duk da cewa ba a samu wata hujja mai gamsarwa kan rahoton farko da ya fito ba.
Comments 1