Gwamnan Benue, Hyacinth Iormem Alia a ranar Juma’a, ya tabbatar wa matasan jihar cewa nan ba da dadewa ba abubuwa za su daidaita a jihar, Daily Post ta rawaito.
Gwamnan ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabi ga matasan, a zagayen Wurukum dake Makurdi, babban birnin jihar yayin da ya dawo daga babban birnin tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Sanda Sun Tsere Lokacin da ’Yan Daba Suka Mamaye Rumfunan Zabe – Wani Shaida Ya Fadawa Kotu
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa wasu matasa wadanda akasari masu tuka babura ne a ranar Juma’a a garin Makurdi, sun haifar da cunkoson ababen hawa a kan titin Food Basket, inda aka yi takun-saka tsakanin ‘yan sanda da wasu jami’an sojojin Najeriya.
Gwamna Alia ya tsaya na wani dan takaitaccen lokaci domin kwantar da hankulan al’umma, inda ya yi jawabi ga matasa tare da ba su tabbacin samar da dabaru masu ma’ana na samawa matasan jihar aikin yi da kuma sanya matasan jihar su yi sana’o’i masu inganci da za su amfanar da al’ummar Binuwai.
Ya jaddada karfafa matasa ta hanyar amfani da ilimin fasaha da horo don ci gaba mai dorewa.
Gwamnan ya kuma yi gargadin a guji cin zarafin jama’a da jami’an tsaro ke yi, ya kuma kara da cewa masu tuka babura a jihar su rika kiyaye doka da oda.
Sannan kuma kada jami’an tsaro su rika muzgunawa ko cin zarafin duk wani dan jihar Binuwai da ke aiki yadda ya kamata domin samun abin rayuwa.
Ya amince da wahalhalun da jihar ke ciki, ya kuma ba su tabbacin cewa nan ba da jimawa ba abubuwa za su daidaita.
A wani labarin kuma, Wani Gwamna a Arewa Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da Shirin Nada Basaraken Gargajiya
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya bayar da umarnin dakatar da shirin nadin wata sarautar gargajiya a karamar hukumar Takum cikin gaggawa.
Umurnin dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da wata kungiya ta bukaci gwamnan da jami’an tsaro da su dakatar da taron nadin sarautar domin gujewa wani yanayi na rashin bin doka da oda a jihar.