Rahotanni na nuna cewa, A shekarar da ta gabata, Adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya kai miliyan 71.1 a fadin duniya saboda tashe-tashen hankula kamar yakin Ukraine da Iftila’in da sauyin yanayi ya haifar kamar ambaliyar ruwan damina a Pakistan, a cewar, wani rahoton da aka wallafa a ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya ruwaito cewa, Cibiyar Kula da adadin masu neman mafaka a Geneva (IDMC) ta ce adadin ya karu da kashi 20 cikin 100 tun daga shekarar 2021, inda ba a taba samun irinsa.
KU KARANTA: An Tsinci Wani Yaro Dan Kano A Kasar Togo, Kwanaki Bayan Bacewarsa
IDMC ta ce kusan kashi uku cikin hudu na mutanen da suka rasa matsugunansu a duniya na rayuwa ne a kasashe 10 da suka hada da Syria, Afghanistan, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Ukraine da kuma Sudan sakamakon rikice-rikicen da suka haifar da gagarumar gudun hijira a shekarar 2022.
Cibiyar ta kara da cewa, Yakin da ake yi a Ukraine ya janyo asarar rayuka kusan miliyan 17 a bara.
Yakin da ake yi a Ukraine ya kuma kara ruruta wutar matsalar karancin abinci a duniya da ya fi shafa ‘yan gudun hijira, inji IDMC.
A wani labarin kuma, Dalilin FG Na Amincewa Da Wasu Ayyuka A Wannan Lokaci – Minista
Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kwangilolin biliyoyin nairori kasa da kwanaki 18 kafin karshen mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Ministan Sufuri Mu’azu Sambo da takwaransa na albarkatun ruwa Sulaiman Adamu ne suka bayyana hakan bayan taron FEC da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.