Daya daga cikin wadanda ake zargin a fashin bakin offa, Ayode Akinnibosun, ya ce, Dakataccen shugaban yan sanda yaƙin da masu aikata laifukan fashi da makami (IRT) Sufeto Janar Abba Kyari ya bashi Naira miliyan 10 da biza domin ya ɓata sunan tsohon shugaban majalisar Dattijai Sanata Bokala Saraki. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a gaban babbar kotu dake Illorin babban birnin jihar Kwara, yayin da aka dawo sauran ƙarar, inda yace kyari yayi masa tayin amma ya yi watsi da shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Kada Ku Zargi Gwamnonin G-5 Idan Sulhu Ya Gagara – Ortom
Akinnibosun, ibikunle Ogunleye, Adeola Abraham, da sauran wasu Biyu na daga cikin wadanda yan sanda ke tuhuma da aikata miyagun laifukka da suka haɗa da fashi da makami, kashe jami’an yan sanda 9 da wasu mutane hadi da riƙe makami babisa ƙa’idaba.
Da yake jawabi ga manema labarai Akinnibosun ya bayyana yadda aka kashe wani daga cikin wadanda ake zargin da fashi da makami Michel Adikwu a gabansa lamarin da ya sanya shi ya amince da ya ɓata sunan Saraki.
Daga nan mai Shari’a Alimat Salman ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa 13 gawatan Febuwairun shekarar nan.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Dake Kamanceceniya da Angalawai (Diphtheria), Ta Hallaka Mutane 25
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa, a ranar Alhamis, ya tabbatar da bullar cutar da take kamanceceniya da angalawai (Diphtheria) mai saurin kisa da aka ce ta kashe mutane akalla 25 a jihar.
Alamomin cutar kisa sun hada da ciwon makogwaro, tari, zubewar yawu, canjin murya, kumburin wuya, rashin numfashi, zazzabi ko warin baki, da sauransu.