Magoya bayan kwallon kafar tawagar kasar Kamaru sun nuna goyon bayansu ga Super Eagles kuma suna sha’awar ganin kasashen biyu sun fafata a wasan karshe a gasar cin kofin Afrika na 2021.
Keimba Agnes Ursule ta ce tana matukar kaunar bangaren Najeriya kuma tana son su buga wasan karshe.
“Ina son yadda Najeriya ke buga kwallon kafa kuma ina son ganin sun kai wasan karshe. Suna da kyau kuma suna da daidaito a tsakanin su. Na kalli wasan sh a talabijin kuma yana da kyau in gan su a ƙasata yanzu, ”in ji ta.
Vincent Ganago, ya yi gargadin cewa idan Najeriya ta hadu da kasarsa a wasan karshe, toh a sa ran soyayya da goyon bayansa ga Kamaru.
“Super Eagles ita ce tawa ta biyu bayan Kamaru kuma zai yi kyau in ga sun kai wasan karshe. Kuma idan za mu yi wasa da su, dole ne su yi rashin nasara,” ya jaddada.
Wani Kuma Mai suna Aliyou Abdallah ya ce yana goyon bayan Najeriya a wasanta na farko da kasar Masar, yayin da daga bisani a jiya yaso Sudan ta doke Super Eagles.
‘A wasan farko na goyi bayan Najeriya da Masar saboda makwabta ne kuma yanki daya ne. Amma a yau (jiya) ina goyon bayan Sudan saboda zan fi son su fiye da Najeriya idan muka hadu a zagaye na gaba,” inji shi.