AFCON 2023: Abin da muke bukata ke nan – Ahmed Musa ya roki ‘yan Najeriya
Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya bukaci ‘yan Najeriya da su basu ‘goyon baya’ a lokacin da za a fara gasar cin kofin Afrika na 2023, AFCON, a karshen wannan makon a kasar Ivory Coast.
A cewar Musa, goyon baya shine kawai abin da mazan Jose Peseiro ke bukata daga ‘yan Najeriya don samun nasara a AFCON.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Katsina Ta Ce Matsalar Hanyoyi Biyu Suka Fi Damunta
Wasan farko na Super Eagles za’a fafata da Equatorial Guinea ranar Lahadi.
Da yake magana da NFF TV, Musa ya ce: “Kowa ya yi farin ciki a sansanin, yana murna, muna jiran mu je Abidjan domin fara gasar.”
Tsohon dan wasan na Leicester City ya kara da cewa, “Sakon da nake da shi ga ‘yan Najeriya shi ne kawai imani da kungiyar, shi ne kawai abin da muke bukata. Tare da goyon bayansu, za mu iya yin nisa.”
Ita kuwa Super Eagles ta sha kashi ne da ci 2-0 a wasan sada zumunta na karshe da suka yi da Guinea