AFCON: NFF ta yabawa Peseiro kan lallasa ƙasar Afirka ta Kudu
Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, Shehu Dikko, ya jinjinawa babban mai horar da ‘yan wasan kasar, Jose Peseiro, bisa jajircewarsa da ya yanke a wasansu da Afrika ta Kudu.
Super Eagles dai ta je bugun daga kai sai mai tsaron gida, domin ta doke kungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta Bafana a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka gudanar a daren Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta shirya yi
Dikko, ya rubuta a shafinsa na X da aka tabbatar, ya ce Peseiro ya aminta da sauran ‘yan wasa a cikin tawagarsa yayin da wasan ya shiga matakai masu muhimmanci.
Ya rubuta: “Na taya @JosePeseiro… Kyakkyawan aiki da babbar girmamawa ✊….
“Koci mara tsoro, kwararre kuma mai kwarin gwiwa ne kawai zai yi karfin gwiwa ya maye gurbin manyan ‘yan wasansa uku da ‘yan wasan tsakiya guda biyu a Osimhen, Simon, Lookman, Iwobi, da Onyeka a wasan kusa da karshe ko a mutu …. yana da amanar aika mai tsaron baya na tsakiya a matsayin wanda zai maye gurbin na 6 don shiga bugun fanareti…. kuma duk sun yi aiki da kyau sosai kuma an sami sakamako mai kyau.
A wani labarin kuma:INEC ta gabatar da satifiket ga wadanda suka yi nasara a zaben cike gurbi na ranar Asabar
A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayar da takardar shaidar cin zabe ga wadanda suka yi nasara a zaben da aka yi a ranar Asabar.
An gabatar da taron ne a hedikwatar INEC dake Abuja.
Wadanda suka samu takardar shedar sun hada da Farfesa Anthony Okorie, zababben Sanata mai wakiltar Ebonyi ta Kudu, Mista Pam Dachungyang, zababben Sanata mai wakiltar Filato ta Arewa da kuma Musa Mustapha, zababben Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas.