Jam’iyyar adawa mafi girma a Ghana ta zabi tsohon shugaban kasar, John Dramani Mahama, a matsayin dan takararta a zaben shugaban kasa na 2024,Africa News ta rawaito.
A karshen mako ne wakilan jam’iyyar NDC suka kada kuri’a a zaben fidda gwani na zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun Ayaba: Wata ‘Yar Najeriya Na Neman Karya Tarihin Gasar Dafa Abinci Ta Duniya
An ayyana Mahama a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu kashi 98.9 na kuri’un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa tsohon magajin garin Kumasi Kojo Bonsu ya samu kashi 1.1 cikin 100.
Mafi akasarin masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce tsohon shugaban kasar ya lashe zaben fidda gwani bisa gogewa da tasirinsa a jam’iyyar adawa.
Kwame Asah-Asante, malamin kimiyyar siyasa a jami’ar Ghana ya ce “An gwada shi kuma ya zo da kwarewa sosai.”
Da yawa daga cikin wakilan jam’iyyar NDC sama da 355,000 ne suka yi dandazo a cibiyoyin zabe 401 a fadin kasar a karshen mako domin kada kuri’a.
“Na yi imanin idan NDC ta karbi mulki, yawancin abubuwan da mu ‘yan Ghana muke so, NDC za ta iya zuwa ta yi mana. Misali kula da ‘ya’yanmu. Daya bangaren ya yi mana alkawari da yawa wanda suka kasa cikawa,” in ji wani dan kasuwa Kafur Addo.
Ya ce ya yi imanin cewa idan NDC ta hau mulki, jam’iyyar za ta cika alkawuran da ta dauka.
Zaben fidda gwanin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke tattaunawa da asusun bada lamuni na duniya IMF, kan tallafin dalar Amurka biliyan 3, domin shawo kan matsalar tattalin arziki, da kuma fuskantar barazanar masu jihadi daga rikicin kasar Burkina Faso makwabciyarta.
Manazarta na ganin cewa, mai yiwuwa Mahama zai yi amfani da matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a yakin neman zabensa na shugaban kasa, kuma wakilai sun amince da iya aikinsa.
“Na yi imani da John Dramani Mahama, ya taba zama shugaban kasa, ya taba zama mataimakin shugaban kasa, kuma shi ma mai sadarwa ne, don haka babu yadda za a yi shugaba mai ci ya yi mana wani abu,” in ji dan kasuwa Joshua Rockson.
“Mun ba shi shekaru takwas yanzu kuma babu wani abu da muke gani. Amma tare da John Dramani Mahama, zai iya juya mana abubuwa. Shi ya sa muka yi imani da shi muka zo mu zabe shi.”
Jam’iyya mai mulki ta shugaba mai ci Nana Akufo-Addo za ta gudanar da nata na zaben a watan Nuwamba, kuma za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 7 ga watan Disambar shekarar 2024.
A wani labarin kuma, Buhari Na Da ‘Yancin Ya Ciyo Bashin Dala Miliyan $800m – Tsohon Kwamishina
Tsohon kwamishinan kudi a jihar Abia, Richard Harrison ya goyi bayan bukatar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman rancen dala miliyan 800 don shirin zuba jari ga talakawa da ‘yan Najeriya masu rauni.
Tsohon Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Umuahia.