Kyaftin din tawagar Super Eagles Ahmad Musa ya gama shirya komatson sa don hadewa da tsohuwar Kano Pillars Kamar yadda Jaridar ACL Sports ta ruwaito.
Dan wasan mai shekaru 28 zai hade da Pillars a wani takaitaccen waadi bayan da ya rasa kungiya ɗaya daga turai da za ta amshe shi.
Yanzu haka dai tuni cinikin dan wasan ya kammala, kawai abin da ake jira shine sanar da cikakken bayanin yause zai diro Najeriya.
Musa yana zaune ne kawai kara zube tun bayan da ya yi bankwana da kungiyar sa ta Al Nassr dake kasar Saudiyya a watan Oktoban bara.
Wannan hadewa da zai yi da tshohuwar Ƙungiyar tashi, na nufin zai sake dawowa sabuwar rayuwa Kenan.
Shi dai Ahmad Musa ya shafe tsawon shekara uku yana murza leda wa Kano Pillars gabannin komawar sa Kungiyar VVV-Venlo dake nahiyar Turai