Karamin ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce samar da abinci wani nauyi ne da ya rataya a wuyan dukkan ‘yan Najeriya.
Ya bayyana cewa kashi 50 cikin kadada miliyan 80 na gonakin noma ya rage ba a noma, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su dasa wani abu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai na majalisar dattawa a ofishinsa da ke ma’aikatar noma ta tarayya Abuja a ranar Litinin.
Ministan ya ce daga cikin batutuwa 8 na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, samar da abinci ne ya fi muhimmanci saboda fa’idojinsa da dama.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin fa’idojin da ake samu akwai yaki da cin hanci da rashawa domin wasu kan shiga gurbatattun rayuwa sakamakon yunwa, kamar yadda wasu ke yi ta dalilin talauci, wanda shi kansa, ana iya magance shi ta hanyar samar da abinci.
Lokacin da kuka tabbatar sun ci sun koshi dabi’ar talakawan Najeriya na cin hanci da rashawa ko aikata laifuka za su ragu.
Ya kamata ‘yan Najeriya su shiga cikin wannan manufa ta hanyar shuka wani abu a duk inda suke.
A wani labarin kumaCAN Ta Jajantawa Al’ummar Jahar Kaduna Akan Abinda Ya Faru A Tudun Biri
Har ila yau, gwamnati ta kuduri aniyar ganin an noma wani kaso mai tsoka na kadada da ba a noma a kasar nan.
Kamar yadda yake a halin yanzu, daga cikin hekta miliyan 70-80 na gonakin da ake nomawa a kasar nan, kadada miliyan 34 ne kawai ake nomawa, wanda hakan ke nufin akwai wadatattun filayen noma da gwamnati da ‘yan Nijeriya za su iya binciko noma da kuma karawa domin tabbatar da samar da abinci a kasar nan,” inji shi