Gwamnatin jihar Benue ta ce za ta bude hanyoyin ruwa da suka toshe domin kaucewa afkuwar ambaliyar ruwa a jihar.
Kwamishiniyar hadin gwiwa, raya birane da karkara, Hon. Joy Luga, ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ke rangadin yankunan da ake fama da ambaliyar ruwa domin sanin irin barnar da ruwan saman da aka yi a jihar ya haddasa.
KARANTA WANNAN: EFCC ta Gurfanar da Wani Matashi a Gaban Kotu Bisa Zargin Sace Miliyan N251.6m
A cewarta, matsalar ambaliyar ruwa lamari ne da ba a saba da shi a jihar Benue.
Luga ta yi gargadi game da gina gidaje a magudanar ruwa, ta kuma shawarci mazauna garin da su rika neman amincewar hukumar raya birane a kodayaushe kafin fara duk wani aikin gini.
Tun da farko, Babban Manaja na Hukumar Raya Birane, Town Planner Mede ya shaida wa kwamishiniyar cewa sassa da dama na garuruwan na cike da ambaliya saboda rashin bin umarnin hukumar.
Don haka ya yi kira ga jama’a da su rika yin gini bisa ka’ida da umarni.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar masu gidaje a Kanshio, Mista Timothy Audu, ya shaidawa kwamishinan cewa al’umma na son baiwa ma’aikatar hadin kai domin bude hanyoyin ruwa da aka toshe.
Kwamishiniyar ta ziyarci wurare da dama a cikin garin na Makurdi domin duba illar mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Shettima Zai Wakilci Shugaba Tinubu a Wani Muhimmin Taro a Cuba
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Laraba ya bar Najeriya domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron shugabannin kasashen G77+China a birnin Havana na kasar Cuba, wanda zai gudana daga ranar 15 zuwa 17 ga watan Satumba.
A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Olusola Abiola ya fitar, ya ce Shettima zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya ciki har da babban sakataren MDD Antonio Guterres a wajen taron.