Sama da Mutum 52 ne su ka rasa rayukan su a Jamhoriyar Niger, ya yin da wasu 34 kuma su ka sami raunuka, dubbunnai kuma su ka rasa gidajen su.
Hakan ya hada da jimulla mutune biyar da su ka mutu tsakanin ranar Talata da Laraba, a Babban birnin kasar dake Niamey, bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, Wanda ya haifar da mummunar asara da kuma sanya daruruwan mutane rasa matsugunan su.
A cewar hukumar kare fararan hula dake kasar ta ce, an sami rahoton ambaliyan ruwa, Wanda ya lalata akalla gine-gine 4,000.
Hakan na nuna cewa, yankuna da dama a kasar ne ambaliyan ruwan ya shafa, tun daga farkon watan Yunin shekarar nan, zuwa yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Garkuwa da mutane: Mutane 8 sun shaki iskar yanci a Ekiti
Babban birnin kasar shine birnin da lamarin yafi kamari, daga cikin sauran buranen dake kasar.
Idan za’a iya tuna wa, ko a shekarar da ta gabata, sai da akalla Mutum 70 su ka mutu, sanadiyar ambaliyan ruwa a jamboriyar Niger.
A wani labarin na daban Amma a Nigeria
Jami’iyar adawa ta PDP reshen Jihar Kano, ta yi Fatali da bukatar yin Murabus din Shugaban jam’iyar ta Kasa Prince Uche Seconds.
Shugaban jam’iyar a jihar Alhaji Shehu Sagagi ne, ya yi Fatali da bukatar yin Murabus din Shugaban jam’iyar ta Kasa, lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai a garin Kano a jiya Laraba.
Sagagi ya ce, ” Muna goyan bayan Shugaban jam’iyar PDP na Kasa, sabida bai yi wani abu wanda ba dai-dai ba, da har za’a bukaci ya yi murabus daga mukamin shi”. Inji shi.
Ya kuma kara bayyana cewa, jam’iyar na da masaniya kan wasu mabobin ta, da ke aiki tare da na jam’iyar APC Mai mulki, domin haifar da rikicin cikin gida a dukkannin matakai na Jam’iyar PDP, bisa kudirin su na ganin kawo rashin dai-dai-to a jam’iyar, domin hana ta karbar Mulkin kasar nan, a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.