Akalla mutum dubu hamsin (50,000, ) ne aka bukaci su bar muhallasu sakamakon barnar da ambaliyar ruwa tayi a birnin Sydney , birni na uku mafi girma a kasar Australiya.
Wannan ya biyo bayan mamakon ruwan saman da aka rinka yi a birnin, inda cikin kwanaki hudu birnin ya samu ruwan saman da ya kamata ya samu na tsawon watanni takwas.
An rufe titina da dama, Yayin da gidage da dama suka nutse, dubban mutane kuma suka kasance babu wutar lantarki a gidagen su.
Ambaliyar ruwan da ta auku a sanadiyar sauyin yanayi a yankin ta kashe fiye da mutum 20 a wannan shekarar, da kuma wasu da dama a yankin Jyankin New South wales.
Al’ummar yankuna fiye da dari ne aka baiwa umurnin tashi da ga gidajensu cikin gaggawa a birnin na Sydney dake kasar Australiya
Wasu mutane dake wurare da suka kai 50 an musu gargadin da su bar muhallasu, kasancerwar da yawa daga cikin manyan magudanan ruwan kasar sun cika.
Kuma yanayin na ci gaba da matsawa yankin Illawarra.
Hukumar kula da yanayi ta kasar tace, An tafka ruwan sama da yawanshi ya kai mili mita 800 a ma’auni karfin ruwa, a Wasu yankunan na birnin New South wales , wanda ya Ninka adadin yawan ruwan saman da birnin London ke samu har sau uku a shekara guda.
Ministan bayar da agajin gaggawa na New South Wales Stephenie Cooke yace har yanzu basu kammala bayar da agajin gaugawa ba.
To sai da an rawaito cewa, ana sa ran ruwan saman ya ragu a birnin Sydney a yau talata, sai dai ana hasashen samun iska mai karfi da zai iya kayar da itatuwa da turakun wutar lantarki.
A yanzu dai mahukunta na ci gaba da gargadin al’ummar da ke wadanan yankunan da su yi gaggawar tashi a yankunan na su, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin ceton wadanda aka baiwa gargadin barin muhallasu kwanaki biyu da suka wuce.