- Gwamnatin tarayya a daren yau 28 ga watan Agustan 2023 ta tabbatar da cewa hukumomin Kamaru sun sako ruwa daga dam din Lagdo
- Ministar ta bukaci gwamnatocin jihohi da al’ummomin da ambaliyar ruwa za ta iya shafa da su fara kwashe ‘yan uwansu da dabbobinsu cikin gaggawa zuwa ga filin da ruwan bai zai shafa ba
- Gwamnatin tarayya za ta samar da matsuguni na wucin gadi da sauran kayayyakin agaji ga wadanda abin zai iya shafa
Gwamnatin tarayya a daren ranar Litinin ta tabbatar da cewa hukumomin Kamaru sun sako ruwa daga dam din Lagdo, The Nation ta rahoto.
Gwamnatin tarayya ta kuma ce ‘yan Najeriya za su fara jin tasirin bude madatsun ruwa nan da kwanaki bakwai masu zuwa.
KARANTA WANNAN: Rikicin Kananan Hukumomin Filato: NULGE ta Tsunduna Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
Ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr. Betta Edu ta bayyana haka a yayin wani taron karawa juna sani da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na farko.
Domin tabbatar da daidaiton yadda ya kamata, Ministar ta ce ma’aikatarta tare da wasu za su yi aiki tare da ofishin mataimakin shugaban kasa da kuma kungiyar gwamnonin Najeriya don tabbatar da dakile illolin da ambaliyar ruwa ke iya haifarwa.
Ministan ta bukaci gwamnatocin jihohi da al’ummomin da ambaliyar ruwan za ta iya shafa da su fara kwashe ‘yan uwansu da dabbobinsu cikin gaggawa zuwa ga filin da ruwan ba zai je wurin ba.
Ta kuma yi nuni da cewa gwamnatin tarayya za ta samar da matsuguni na wucin gadi da sauran kayayyakin agaji ga wadanda abin zai iya shafa.
Ta ce: “Mun taru ne kan shugaban kasa bayan jawabai da na gabatar a FEC a yau kan bude dam din Lagdo na Kamaru wanda tuni aka bude yayin da muke magana kuma ana sa ran nan da kwanaki bakwai masu zuwa za mu fara ganin tasirin bude wannan dam a Najeriya.
“A halin yanzu muna da aiki kai tsaye daga shugaban kasa na tabbatar da shirye-shiryen da ya kamata dangane da sakamakon dam din da aka bude a kasar Kamaru kuma shi ya sa ake gudanar da wannan taro na hadin gwiwa a daren yau don taimakawa Najeriya yadda ya kamata.
A wani labarin kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bada Tallafin Karatu Ga Ɗalibai 628 a Jami’ar BUK
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tallafawa dalibai 628 daga yankin Sanatan Kano ta Arewa domin samun gurbi a Jami’ar Bayero Kano BUK
Mataimakin Shugaban Majalisar ya dauki nauyin shirin ne domin tallafa wa al’ummar mazabarsa don ci gaba da karatunsu a manyan makarantun kasar nan
Wannan karimcin ba na daliban BUK ba ne kawai, duk dalibin Kano ta Arewa da ke karatu a Najeriya zai ci gajiyar wannan shirin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a kokarinsa na taimakawa dalibai daga yankin Sanatan Kano ta Arewa ya bada tallafin karatu ga dalibai 628 a Jami’ar Bayero Kano (BUK).
Sai dai daliban da aka zabo daga mazabar sanatan Kano ta Arewa, inda dan majalisar ke wakilta, an ba su Naira 50,000 kowanne.