- Hukumar NEMA ta bawa mutanen da basu gaza 9000 ba da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe tallafi
- An kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar taron dake gidan gwamnatin jihar.
- An yi kira ga duk wadanda suka amfana da su yaba tare da mayar da hankali wajen yin amfani da kayayyakin yadda ya kamata tare da kaucewa sake sayar da su
Yanzu haka dai mutanen da basu gaza 9000 ba da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe ne za su ci gajiyar shiga tsakani don dakile mummunan bala’in ta hanyar agajin gaggawa na rayuwa na musamman na kasa (SNELEI) wanda Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta aiwatar.
Gwamnan jihar Mai Mala Buni ne ya kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar taron dake gidan gwamnati a Damaturu.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Kwara ta Tabbatar da Sunayen Kwamishinonin da Gwamna Ya Aike Mata
Mai Mala Buni ya bayyana cewa, shirin na SNELEI yana da nufin tallafa wa Najeriya na dogon lokaci daga bala’in ambaliyar ruwa na shekarar 2022 da kuma yunkurin dawo da zaman lafiya da tattalin arziki mai dorewa a kasar daga kalubalen da ake fuskanta na kawar da tallafin man fetur da kuma yawan kudaden da aka samu na hauhawar farashin kayayyaki, kamar yadda Tribune Online ta rawaito.
An raba kayan noma da na gida ga wadanda ambaliyar ta shafa tare da lura da cewa, SNELEI kunshin tallafi ne da ke dauke da kayan abinci, da kayayyakin tallafi na rayuwa, ciki har da ingantattun iri da kuma kayan aiki, wanda zai taimaka matuka wajen toshe guraben da aka samu ta hanyar kawar da tallafin, ta yadda za a bunkasa kudaden shiga na gidaje da bala’in ambaliyar ruwa na shekarar 2022 ya shafa.
Gwamnan ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya ta hannun hukumar NEMA bisa bullo da shirin domin kawo dauki ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Yobe a shekarar 2022.
A cewarsa, “Tsarin SNELEI na Mataki na 1, wanda zan fara nunawa a yau, ya shafi sama da masu cin gajiyar shirin su kimanin 9000 daga cikin 24,640 da aka yiwa rajista.”
Ya bayyana cewa, “Masu cin gajiyar da suka rage a dukkanin kananan hukumomi 17, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ce ta tantance wadanda za su ci gajiyar wannan kunshin”.
Mai Mala Buni ya yi kira ga duk wadanda suka amfana da su yaba tare da mayar da hankali wajen yin amfani da kayayyakin yadda ya kamata tare da kaucewa sake sayar da su.
Tun da farko a takaitaccen jawabin babban daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ahmed Mustapha Habib, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da daukar matakin ne domin taimakawa marasa galihu a fadin kasar nan da wadanda ambaliyar ruwa ta shafa domin tallafa musu cikin gaggawa.
Shugabar wacce ta samu wakilcin wata babbar jami’a daga hukumar, Hajiya Bintu Awana Aliyu, ta bayyana cewa, an tantance magidanta 66,884 da aka yi niyyar zasu ci gajiyar tallafin na musamman a fadin jihohin kasar nan 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Ta shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin na jihar Yobe da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata domin inganta zamantakewa da tattalin arzikinsu.
Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun yaba da wannan karimcin na gwamnatin tarayya da kuma na jihar Yobe, inda suka ce kayayyakin za su yi matukar taimaka musu wajen dakile abin da suka rasa a bala’in daya afku.
Sun kuma bayyana kwarin gwiwar cewa za su iya sake samun rayuwa, bayan da suka rasa hanyoyin rayuwa a lokacin bala’in.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: IGP Egbetokun Ya Ziyarci Rundunar ‘Yan Sandan Legas
Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya kai ziyarar gani da ido a hedikwatar ‘yan sandan jihar Legas
Ziyarar ita ce ta farko tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada shi a matsayin IGP
IGP ya samu tarba daga Kwamishinan ‘yan sandan jihar
Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya kai ziyarar gani da ido a hedikwatar ‘yan sandan jihar Legas da ke Ikeja, babban birnin jihar.
Ziyarar ita ce ta farko tun bayan da shugaba Bola Tinubu ya nada shi a matsayin IGP.