Adadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta yi barna a yankuna da dama na kasar Kenya ya kusan kaiwa zuwa 120, kamar yadda wani jami’in gwamnati ya bayyana a ranar Talata.
Fiye da gidaje 89,000 kuma sun rasa matsugunansu kuma suna samun mafaka a sansanoni sama da 112, in ji babban jami’in ma’aikatar cikin gida Raymond Omollo a cikin wata sanarwa.
Karanta nanHajji 2024:An Bukaci Maniyyata A Jahar Sokoto Da Su Gaggauta Biyan Kudadensu
Kenya da makwabtanta na Afirka Somaliya da Habasha na fama da ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama mai alaka da yanayin El Nino.
Ambaliyar ruwan tana kara ta’azzara matsalar jin kai a yankin a daidai lokacin da ake bullowa daga fari mafi muni cikin shekaru arba’in da ya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa.
Omollo ya ce kananan hukumomi hudu a gabashin Kenya ne suka fi fama da bala’in yayin da wasu 10 ke cikin shirin ko ta kwana.
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya jagoranci taron gaggawa na majalisar ministocin kasar kan bala’in a ranar Litinin, inda ya yi alkawarin sakin biliyoyin kudin Kenya (miliyoyin daloli) ga yankunan da lamarin ya shafa.
A wata sanarwa da ofishinsa ya fitar bayan taron ya ce ‘yan kasar Kenya 76 ne suka halaka sannan sama da gidaje 35,000 aka tilastawa barin gidajensu.
A wani labarin kumaBabu Wanda Ya Taba Satar Kudi A Nijeriya Kamar Diezeni-TY Danjuma
Hazo mai yawa da aka samu, ya haifar da ambaliyar ruwa da ta haifar da asarar rayuka, da raba iyalai, barkewar cututtuka, lalata kayayyakin more rayuwa da dukiyoyi, da kuma tsawaita katsewar wutar lantarki a fadin Kenya da sassa da dama. na yankin Gabashin Afirka,” in ji shi.
Shugaba William Ruto da yake zantawa da manema labarai ya bayyana wannan lamari a matsayin wani babban bala’i da ya tunkaro kasar dake gabacin Afirika,inda yayi alkawarin bayar da tallafin kudade ga iyalan da abin ya shafa.