Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 50, ta raba Mutane da yawa daga mahallin su a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 50 tare da raba wasu da dama da muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye wasu sassan jihar.
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sani Yusuf, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Manema Labarai a Dutse, ya ce ambaliyar ta kuma lalata dubban gidaje a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Bindiga sun kai hari Makaranta, sun kashe malami a Nasarawa
Yusuf ya bayyana cewa lamarin ya tilastawa Mazauna Jigawa da dama neman mafaka a wasu wurare da suka haɗa da gine-ginen Gwamnati.
An tattaro cewa Gwamnatin Jihar ta ɗauki mutanen da suka rasa matsugunansu a sansanonin wucin gadi 11.
Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su ‘yan kauyen Balangu ne inda gidaje akalla 237 suka nutse a karkashin ruwa tare da lalata wasu mutane hudu.
“Muna da ‘yan gudun hijira da yawa a sansanonin wucin gadi 11. A Balangu kadai, an lalata gidaje 237, kuma mutanen da ke zaune a sansanin na wucin gadi ne,” in ji Yusuf.
“Mutane hudu kuma sun mutu a wannan kauyen, bayan mutane shida a Kafin Hausa. Don haka, idan ka zagaya jihar, mun yi asarar kimanin mutane 50 a ambaliyar ruwa a yanzu. Ko a jiya (Asabar) mutane bakwai daga gida daya suka mutu.”