Rahotanni sun bayyana cewa mutane 10 ne suka mutu tare da lalata gidaje sama da 200 da tituna a unguwannin dake babban birnin jihar Katsina da kuma karamar hukumar Bindawa ta jihar sakamakon mamakon ruwan sama da aka shatata.
A cewar mazauna yankin da lamarin ya shafa a cikin birnin Katsina, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya fara sauka ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Talata, inda har zuwa daren ranar.
KARANTA WANNAN: CAN Ta Yi Ta’aziyyar Mutuwar Wasu Fastoci Tare Da Rokon FG
Majiyar mu ta rawaito Ungwan Sabuwa, tare da kofar Kaura an ce ruwan sama ya fi kamari a cikin birnin Katsina.
Lokacin da jaridar Vanguard ta ziyarci unguwar tun da farko, an ga mazauna unguwar suna kokarin kwashe kayansu daga gine-ginen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su.
Mai ungwa na yankin, Alh Yunusa Suleman Rico ya shaidawa manema labarai cewa mutane 10 ne suka mutu a iftila’in, ciki har da wani jariri da ba a gano gawar sa ba.
A cewar Rico, bala’in ya faru ne sakamakon rashin magudanar ruwa a unguwar da lamarin ya shafa, inda suka to she suka hana ruwan fita da ke kwarara daga Kofar Kaura.
Hakazalika, a karamar hukumar Bindawa ta jihar Katsina rahotonni sun bayyana cewa sama da gidaje 200 ne aka ce sun ruguje sakamakon ruwan sama da aka yi a ranar Talata.
A halin da ake ciki, wata sanarwa da Ibrahim Kaula Mohammed, babban sakataren yada labarai na gwamnan Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ya fitar, ta nuna cewa mutane biyu ne kawai suka mutu sakamakon bala’in da ya afku a cikin birnin Katsina.
Gwamna Radda ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da iyalansu, inda ya ce tuni aka fara kokarin shawo kan lamarin tare da hana afkuwar irin haka nan gaba.
Sanarwar Da Aka Fitar Ta Ce A Wani Bangare:
“Ambaliyar ta haifar da cikas da barna, ta yi tasiri ga rayuwar yau da kullun na mazauna yankin tare da haifar da damuwa a cikin al’umma.
“Wani abin takaici ma wasu mutane biyu daga garin Sabon Ungwa da ke cikin garin Katsina sun rasa rayukansu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.
“Gwamna Radda, wanda ya shahara da jajircewarsa, ya dauki matakin gaggawa don tallafa wa mazauna yankin da kuma hana afkuwar irin haka nan gaba.
“Tare da jajantawa wadanda lamarin ya shafa, ya yi alkawarin gano musabbabin ambaliya tare da aiwatar da matakan dakile hadurran da ke tattare da ruwan sama mai yawa da kuma rashin ababen more rayuwa.
A bisa wannan alƙawarin, Gwamnan ya umarci Mataimakin Gwamnan da ya haɗa hannu da ƴan kwangilar da ke da alhakin gina hanyoyin mugudanun ruwa don bincikar musabbabin wannan bala’in.
“Da yake la’akari da gaggawar lamarin, Gwamna Radda ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen magance matsalolinsu cikin gaggawa.
“Ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin da abin ya shafa, da masana, Gwamnan na da burin samar da mafita mai dorewa da za ta kare al’umma daga aukuwar ambaliyar ruwa a nan gaba.
“Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin koyo daga wannan lamari mara dadi da kuma amfani da shi a matsayin wata dama ta karfafa shirye-shiryen bala’o’in jihar da hanyoyin mayar da martani.
“Ya kuma jaddada bukatar samar da tsayayyen tsari, da inganta kayayyakin more rayuwa, da ingantattun dabarun kula da su domin tabbatar da tsaro da walwalar daukacin mazauna jihar Katsina.
A karshe, Gwamna Radda ya jajantawa wadanda iftila’in ya shafa da iyalansu da ambaliyar ruwan ta shafa.
“Saurin mayar da martani da jajircewarsa wajen ganin an shawo kan lamarin ya nuna jajircewarsa wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar Katsina.
“Hanyar da Gwamnan ya bi don hana faruwar al’amura a nan gaba ya jaddada kudurin gwamnatinsa na ba da fifiko ga tsaron dukkan mazauna yankin.”
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Jiga-Jigan Jam’iyyar APC Sun Ziyarci Tinubu Bayan Shugabannin NASS Sun Yi Gaban Kansu
A halin yanzu dai shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu yana ganawa da shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu da sakataren jam’iyyar Dr Iyiola Omisore a fadar gwamnatin da ke Abuja.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa mutane biyun sun isa fadar Aso Rock Villa ‘yan mintuna kadan kafin karfe 5 na yamma.