Kimanin gidaje 116 ne ambaliyar ruwa ta shafa, bayan ruwan sama da sanyin safiya ya mamaye rukunin gidaje na Trademore dake kan titin filin jirgin sama a Abuja.
Babban Darakta Janar na Babban Birnin Tarayya, FCT, a Hukumar Ba da Agajin Gaggawa, Dr Abbas Idriss ya jaddada cewa ba a rasa rai ba, sakamakon ambaliyar.
KU KARANTA: Fasa Qwaurin Man Fetur Ya Ragu, Bayan Cire Tallafinsa
An dai nuna damuwa tun da farko cewa an rasa akalla rai guda a lamarin.
To sai dai Idriss ya yi kira ga mazauna yankin da aka gina gidajensu a tashar ruwa da su kaura, yana mai jaddada cewa ambaliyar ruwa a Estate Trademore ta faru ne sakamakon yawan ruwan saman da aka samu.
Nkechi Isa, shugabar hulda da jama’a ta hukumar ta FEMA ta ruwaito maigidan nata yana cewa yankin na Trademore yana fuskantar matsalar ambaliya.
Idriss ya bayyana cewa, Ambaliyan ya ragu, a don haka ya godewa masu ruwa da tsaki da mazauna yankin saboda kokarin da suke yi da hadin gwiwa a Estate Trademore don tabbatar da cewa ba a rasa rai ba.
Hukumar Kula da gudanar Ruwa ta Najeriya, NIHSA, ta yi hasashen ambaliyar ruwa a FCT.
Ta shawarci mazauna garin da su rika amfani da lambar kira ta kyauta a gaggawa ta 112 a duk lokacin da lamarin ya faru.
A wani labarin kuma: Eid-l-Kabir: Yadda Farashin Shanu Ke Cigaba Da Faduwa Warwas A Kasuwanni
Yayin da bikin Eid-el-Kabir da akafi sani da Babbar Sallah ke karato wa, masu sayar da shanu a cikin birnin Bauchi sun ce kasuwar ba ta bunkasa kamar yadda ake tsammani ba
Dillalan sun ce karancin sayen shanun bai rasa nasaba da yanayin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.
Abubakar Bura Adamu, dillalin shanu a wata kasuwar shanu ta zamani da ke kusa da tashar mai ta AY Makama, ya shaida wa Majiyar mu cewa mutane za su so su saya, amma ba za su iya yin hakan ba sai da kudi a hannunsu.