Ambaliyar Ruwa ta shafi Mutum 24,714 a Abuja
Hukumar kula da babban birnin tarayya, FCTA, ta ce mutane 24,714 ne ambaliyar ruwa ta shafa a wasu sassan babban birnin kasar a shekarar 2022.
A karshen mako ne babban daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta babban birnin tarayya Abuja, Abbas Idriss ya bayyana hakan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Dan Wasan Man United Ighalo Ya Sanar Da Gwaninsa A Fadin Duniya
Haka kuma, mutane 2,972 ne suka rasa matsugunansu a AMAC, sannan gidaje 102 sun lalace, lamarin da ya ceci rayuka 9,813.
A cewarsa, a karamar hukumar Abuja, AMAC, mutane 20,376 ne abin ya shafa, sai kuma 2,058 a karamar hukumar Bwari. A lokaci guda kuma, majalisar yankin Abaji ta sami rahoton kararraki 2,280.
“A karamar hukumar Bwari, ambaliyar ta shafi mutane 2,058 a Dutse Makaranta ta hannun ‘yan sanda; a karamar hukumar Abaji, mutane 2,280 ne abin ya shafa a mahauta da ke bayan Sarkin Pawa.”
A wani labarin kuma: ABU Zaria Na Shirin Hada Gwuiwa Da Kasar Saudiyya
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya na shirin kafa wata cibiya a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, a wani bangare na ayyukan ci gaban da cibiyar ta ke yi don bunkasa shirye-shiryenta na digiri na biyu a fadin duniya.
Shugaban jami’ar, Farfesa Kabiru Bala, wanda ya bayyana haka a lokacin da mataimakin shugaban jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA), Dokta Aminu Ado, ya kai masa ziyara a karshen mako, ya bayyana cewa ABU ya kafa cibiyar a Dubai.