Ambaliyar Ruwa Ta Yi Awon Gaba Da Yara 2
An bayar da rahoton mutuwar yara biyu a jihar Anambra sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta afku a garin Nkwele Awka da ke karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.
Yaran ‘yan tsakanin shekaru hudu zuwa bakwai sun rasa rayukansu a wurare biyu daban-daban a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Nijar Ta Yanke Wa Ofishin Jakadancin Faransa Ruwa Da Wuta
Ambaliyar ruwan ta tafi da daya daga cikin yaran a lokacin da yake zubar da shara a gabar ruwan, yayin da daya kuma ya tafi da shi a kokarin tattara silifas dinsa da ambaliyar ta kwashe.
Daya daga cikin mazauna yankin mai suna Ify, ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta aike ta domin ta je ta zubar da shara a lokacin da ruwa ya kama ta.
“Tana zuba shara a cikin magudanar ruwa sai kafarta ta zame kwatsam sai ta fada cikin magudanar ruwa kuma ruwan ya dauke ta,” in ji Ify.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, ya ce ba a kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar ba.
Sai dai ya bayyana lamarin a matsayin tsantsar fitina, yana mai ba da tabbacin ci gaba da hadin gwiwar rundunar da gwamnati don inganta tsaro a jihar.
“Wannan mummunan bala’i ne na muhalli amma muna ci gaba da aiki tare da gwamnati don tabbatar da an inganta tsaro,” in ji shi
A wani labarin kuma:Babu Dokar Da Tace Sai Na Kammala Bautar Kasa Zan Iya Zama Minista-Musawa
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya sake kokawa kan cece-kucen da ya biyo bayan tarihin karatun shugaba Bola Tinubu.
Atiku, wanda a halin yanzu yana roƙo ga wata kotun Amurka da ta umarci Jami’ar Jihar Chicago ta yi karin haske kan rashin daidaito a cikin takardar shedar da ta baiwa Shugaba Tinubu, ya ce matukar ba a yi karin haske ba, abu ne mai wahala, don fahimtar tafiyar karatun tsohon gwamnan jihar Legas.