Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu ‘yan takarar shugaban kasa a lokacin tunkarar zaben shekarar 2015 ya taimaka matuka wajen samun nasarar zaben cikin kwanciyar hankali.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kar Ku Kawo Cikas Ga Kidayar Jama’a A Kudu Maso Gabas, NPC Ga IPOB
Don haka ya bukaci dukkan wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben 2023, da magoya bayansu da su yi biyayya ga abin da ya kunsa.
Ya nuna farin cikinsa da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta farko da ‘yan takarar shugaban kasa suka yi a zaben 2023, tun da farko a wani taron na daban a ranar Alhamis.
Ya ce an yi hakan ne da nufin ganin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da magoya bayansu su gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana, ba tare da kalaman kabilanci da addini da na kiyayya da za su iya kawo cikas a zabukan da ke tafe ba.
“Lokacin da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta farko na da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da yakin neman zaben jam’iyyun siyasa a kasar.”
“Shirye-shiryen da NPC ta yi abin yabawa ne saboda wannan yunƙurin zai tabbatar da kamfen ɗin da ya shafi batutuwa.”
“Ina sa ran shiga kashi na biyu na yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa a watan Janairun 2023.”
“Idan za ku iya tunawa ni da shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan mun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa ta farko kafin zaben shekara 2015.”
“Ina da yakinin cewa hakan ya taimaka matuka wajen samun nasarar zaben shekarar 2015 cikin kwanciyar hankali.”
“Ina fata cewa kwamitin zaman lafiya na kasa ya ci gaba da wannan muhimmin aiki bayan 2023,” in ji shugaban.
Buhari ya nanata cewa za a iya gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da luma.
Ya kara da cewa rattaba hannu kan dokar zabe ta 2021 da aka yi wa kwaskwarima tare da wasu muhimman tsare-tsare ya jaddada kudirinsa na ganin an gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.
Don haka ya bukaci masu ruwa da tsaki da su gudanar da ayyukansu ta hanyar da za ta tabbatar da gudanar da zaben 2023 cikin nasara da kuma mika mulki ba tare da wata matsala ba daga gwamnati ta hanyar dimokuradiyya zuwa waccan gwamnati.
Abubakar wanda ya bayyana wa shugaban kasa ayyukan kwamitin na tunkarar zaben 2023, ya ce sun gana da masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da hukumar zabe mai zaman kanta da shugabannin hukumomin tsaro.
Ya tabbatar da cewa tarurrukan sun kara tabbatar da shirye-shiryen masu ruwa da tsaki na gudanar da zaben cikin nasara.
Tsohon Shugaban kasar ya shaida wa shugaban kasar cewa an kara yawan mambobin kwamitin domin kawo wasu ”matasa masu hankalin”.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa kwamitin zai yi iya kokarinsa don ganin cewa dukkan ‘yan siyasa sun cika abin da ake bukata.
Shugaban NPC ya kuma yaba wa shugaban bisa yadda ya sha nanata kudurinsa na yin adalci a zaben 2023, musamman a wajen halartar taron kasa da kasa.
Ya lura da farin ciki cewa zabukan fitar da gwanin da aka yi a jihohin Anambra, Ekiti da Osun sun tabbatar da jajircewar shugaban kasa na yin zabe mai inganci ba tare da wani tashin hankali a kasar ba.
Mambobin kwamitin zaman lafiya na kasa su ne Abubakar, shugaba; Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmi; John Cardinal Onaiyekan; Alhaji Aliko Dangote da Farfesa Ameze Guobadia.
Sauran su ne; Sam Amuka; Mai shari’a Roseline Ukeje mai ritaya; Farfesa Ibrahim Gambari; Bishop Mathew Kukah; Lt.-Janar mai ritaya. Mathew Luther Agwai da Mista Femi Otedola.
Alhaji Ahmed Yayale; Madam Idayat Hassan, John Momoh; Sani Suleiman Atsu da Attah Barkindo, shugaban sakatariyar NPC su ma mambobin kwamitin.NAN.
A wani labarin kuma, Sarauniya Elizabeth Ta Mutu Ne Saboda Tsufa, Takardar Shaida Ta Bayyana Hakan
Sarauniya Elizabeth ta biyu ta mutu ne saboda “tsufa” da karfe 3:10 na yammacin ranar 8 ga watan Satumba, a cewar takardar shaidar mutuwarta da aka fitar ranar Alhamis, ko kuma kusan sa’o’i uku da rabi kafin a sanar da duniya labarin.
Sarauniyar mai shekaru 96 ta mutu a gidanta na Balmoral Castle a cikin tsaunukan Scotland.