Ɗalibin wanda aka ƙalubalantar, ya kasance yana da jin kunyar mata sosai, hakan ne yasa aka saka masa wannan gasar domin ana ganin ba zai iya ba.
Sai dai jarumin ya bawa kowa mamaki ganin yadda yaje har gabatanta ya kuma yi tsalle a dai dai lokacin da take tafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Amarya Taƙi Yadda A Yi Party A Lokacin Bikinta, Sai Dai Tasa Anyi Tilawar Al Qur’ani Mai Tsarki Domin Neman Albarkar Allah Ta’ala
Hakan ya faru ne a ɓangaren wajen kwanan ɗalibai na jami’ar da Ghana, inda dukkanin ɗaliban maza da mata suka tsaya suna kallon yadda zata kasance tsakanin saurayin da kuma budurwar.
Sai dai lokacin da ya isa inda budurwar take ya kuma yi tsallen, take wajen ya karaɗe da ihu da kuma shewa, ana ta dariya maza da mata.
Sai dai kuma bai ce mata komai ba ita ma kuma bata ce masa komai ba ya juyo ya dawo inda ita kuma ta cigaba da tafiya abinta.
SHIGA NAN DOMIN KALLON BIDIYAN SAURI MAI JIN KUNYAR MATA
Fefen bidiyon wannan saurayi mai jin kunyar matan ya karaɗe lungu da saƙo na kafafen yaɗa labarai da dama, cikinsu har da Facebook inda bidiyan ya samu makallata sama da dubu biyar 5000, inda kuma sama da mutane ɗari biyar suka bayyana ra’ayoyinsu akai.
Wasu ganin cewar bai kamata ya juya ya tafi ba ba tare da yayi mata magana ba.
Wasu kuma ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin suna ganin akwai alamun har yanzu bai daina jin kunyar matan ba.
A WANI LABARIN KUMA: Wata Amarya Ta Bayar Da Umarnin Yin Tilawar Al Qur’ani a lokacin Bikin ta.
Amaryar ta zaɓi a yi Tilawar Al Qur’anin ne kasancewar ita Mahaddaciyar Al Qur’ani mai tsarki ce.
Ta ƙara da cewar, ta zaɓi ayi tilawar Al Qur’anin saboda neman Allah ya sanya albarka a bikin nata tare da rokon Allah ya azurtata da ‘ya’ ya nagartattu wanda suma zasu zama mahaddata Al Qur’ani mai tsarki.
Amaryar ta kuma shaidawa majiyarmu cewar bata da burin yin shalwoliya ko party a bikin nata, hakan yasa ta shirya Tilawar Al Qur’anin a madadin party.
Bidiyon Tilawar ya wanda @bintumtas ta wallafa a shafin sada zumuntar zamani na TikTok ta wallafa ya kuma zagaya lungu da kuma saƙo na sauran kafafen sada zumunta daban daban inda da yawa daga cikin waɗan da suka bibiyi labarin suka yi wa amaryar fatan alheri a zaman auren nata.
Wasu kuma na cewa ya kamata mata su kwaikwai yi amaryar idan shagalin bikin su yazo ko Allah ya sakawa bikin nasu albarka.